Rupert Murdoch da dansa a gaban majalisar dokokin Birtaniya

James Murdoch da Rupert Murdoch Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption James Murdoch da Rupert Murdoch

Babban mai kamfanin kafofin watsa labarai da ke cikin mafiya girma a duniya, Rupert Murdoch, ya ce yau ce ranarsa mafi nadama a rayuwarsa, a yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dokokin Birtaniya, mai bincike a kan zargin abin kunyar da 'yan jaridarsa suka tabka.

Dan Mr Murdock, James, wanda ya bayyana tare da shi, ya bayyana matukar nadama da neman afuwa daga mutanen da aka saurari ko kalli sakonnin wayoyinsu ba kan ka'ida ba.

Jaridarsa ta News of the World, wadda wannan batu ya jawo rufe ta, ita ce ta tabka wannan abin kunya.

Dan sanda mafi girman mukami a Biritaniya kuma ya fuskanci tambayoyi daga kwamitin majalisar dokokin, a kan abin kunyar na saurare da leken sakonnin wayar wani da kuma cin hanci, a katafaren kamfanin kafofin watsa labarai na Rupert Murdoch.

Paul Stephenson - wanda ya yi murabus shekaranjiya Lahadi - ya ce lokacin da ya karbi jagorancin 'yan sandan birnin London, bai da kokanto a kan cewa an yi bincike maras inganci a kan abin kunyar.

Shi ma mataimakin Paul Stephenson, watau John Yates, wanda yayi murabus jiya a kan abun kunyar, ya amsa tambayoyi a yau din daga 'yan majalisar dokokin Birtaniyar.