Holland na da laifi a kashe-kashen Srebenica

Taswirar Bosnia
Image caption Taswirar Bosnia

Alkalan kotun daukaka kara a kasar Holland sun yanke hukuncin cewa, kasar ce ke da alhakin mutuwar wasu musulmi uku, bayan faduwar garin Srebrenica a 1995.

Sojojin kasar Holland dake aiki karkashin Majalisar Dinkin Duniya, su ne a lokacin ke lura da yankin da aka ayyana a matsayin tudun-mun-tsira na majalisar, a lokacin yakin Bosniyar.

Kotun ta ce bai dace ba dakarun na Holland su mika mutanen ga sojan Sabiyawan Bosnia, bayan faduwar garin na Srebenica.

Musulmi dubu takwas ne maza, manya da kananan yara aka kashe, bayan da dakarun Sabiya suka kame yankin.

Kasar ta Holland dai ta sha musanta cewa ita ke da alhakin mutuwar mutanen.