An fitar da Ratko Mladic daga kotu

Ratko Mladic Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ratko Mladic ya yi ta yiwa alkali gatse yayin zaman kotu

An yi waje da tsohon jagoran sojojin Sabiyawan Bosniya, Ratko Mladic, yayin wani zama na kotu bayan sun yi sa-in-sa da alkalin.

Alkalin ya bayar da umurnin fitar da Janar Mladic ne bayan ya yi ta katse masa hanzari.

A madadinsa kuma, kotun ta amsawa Mista Mladic cewa ya musanta aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa, bayan ya ki yin hakan da kansa.

An dai tuhumi Mista Mladic ne da aikata laifuffukan da suka hada da kisan kare-dangi a lokacin yakin Bosniya a tsakanin shekarar 1992 zuwa 1995.

Tun a farkon zaman kotun dai Mista Mladic ya yi ta yunkurin yin magana amma Mai Shari'a Alfons Orie ya umurce shi ya yi shiru har sai an ba shi umurnin yin magana.

Alkalin ya kuma yiwa Mista Mladic fada saboda yadda ya ke magana ba tare da an ba shi umurni ba da kuma yin magana da masu wadanda suka je kotun don kallon yadda shari'ar ke gudana.

Daga nan ne sai Mista Mladic ya ki amsawa ko musanta zargin da ake yi masa, bayan kotu ta ki amincewa da bukatar da ya gabatar ta musanya lauyan da kotu ta zaba masa da wanda shi ya zaba da kansa.

Alkalin dai ya ki amincewa da bukatar Mista Mladic ne saboda, a cewarsa, Mladic din bai shigar da bukatar a kan lokaci ba.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Adadin mutanen da aka tuhuma kawo yanzu dangane da yakin Bosniya

Lokacin da Mai shari'a Orie ya fara karanta tuhume-tuhumen sai Mista Mladic ya fara ihu yana cewa: "a'a, a'a, ni ban zan saurare ka ba ba tare da lauya na ba", sannan ya cire na'urar sauraron da ya ke jin fassarar kalaman alkalin.

Mista Mladic ya kara da yiwa alkalin tsawa yana cewa, "Waye kai da za ka hana ni numfasawa?"

Jim kadan kafin jami'an tsaro su fitar da shi, Mista Mladic ya dubi alkalin yana ihu da cewa "Wacce irin kotu ce wannan da za ka kakaba min lauya?"

Bayan fita da shi ne sai alkalin ya karanta tuhume-tuhumen goma sha daya, ciki har da kisan kare-dangi, sannan ya musanta aikata su a madadin Mista Mladic.