An yanke cibiyar kasar Sudan ta Kudu

An daga tutocin Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Da misalin karfe goma sha biyun dare agogon can aka daga tutocin Sudan ta Kudu

A hukumance yanzu haka sabuwar kasar Sudan ta Kudu ta fara wanzuwa, sakamakon ballewar da ta yi daga kasar Sudan bayan tafka yakukuwan basasa biyu a cikin shekaru fiye da hamsin.

A watan Janairu ne dai fiye da kashi casa'in cikin dari na al'ummar kasar ta Sudan ta Kudu suka kada kuri'ar amincewa da samun 'yanci daga Sudan.

A birnin Juba, inda wani agogo ya kirga dakikoki zuwa sha biyun dare da cewa "Muna Taya Sudan ta Kudu Murna", jama'a na can suna ta wake-wake, da kade-kade, da raye-raye.

Ita dai wannan sabuwar kasa tana kuma cikin kasashen da suka fi talauci a duniya, sannan kuma akwai dalilai da dama da ka iya tsunduma ta cikin wani yanayi na fada da Arewa.

Gwamnatin Sudan da ke Khartoum dai ta amince da kasar Sudan ta Kudu, ta kuma bayyana cewa mutanenta da ke arewa sun daina zama 'yan kasa a arewar.

Har yanzu dai bangarorin biyu ba su amince da hakikanin iyakokinsu ba, kuma a 'yan kwanakin nan an samu tashe-tashen hankula a yankunan kan iyakar kasashen.