An saki Strauss-Kahn ba tare da beli ba

Dominique Strauss-Kahn Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dominique Strauss-Kahn ya fito daga kotu yana murmushi

An dage daurin talalar da aka yiwa tsohon shugaban Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF), Dominique Strauss-Kahn, sannan an mayar masa kudinsa, dala miliyan shida.

An ce masu shigar da kara sun amince cewa a saki Mista Strauss-Kahn a bisa sharadin yarda da shi, wato ke nan abin da ake bukata kawai shi ne ya yi alkawarin zai bayyana a kotu.

An zarge shi ne da laifin farwa wata ma'aikaciyar otal a New York da nufin yin lalata da ita ranar 14 ga watan Mayu.

Sai dai an bayar da rahoton cewa shari'ar na gab da rugujewa bayan da aka nuna matukar shakku game da gaskiyar matar da ta ke zargin sa.

Ranar Juma'a ne dai dan siyasar na kasar Faransa mai shekaru sittin da biyu—wanda ake ganin yana kan gaba a cikin 'yan takarar shugabancin kasar Faransar—ya bayyana a gaban kotu a birnin New York.

Bayan ya auna bayanan masu shigar da kara daga ofishin antoni janar na yankin Manhattan, alkalin ya janye tsauraran sharuddan da aka gindaya na baiwa Mista Strauss-Kahn beli; sai dai ya bayar da umurnin a ci gaba da rike fasfon Mista Strauss-Kahn din saboda kar ya samu damar fita daga Amurka.

Daga cikin bayanan da aka gabatar a gaban kotu har da bayanin cewa ma'aikaciyar otal din ta bayar da shaidar zur a gaban masu taimakawa alkali yanke hukunci, inda ta gaza fadar cewa kafin ta sanar da na gaba ita cewa an tursasa ta sai da ta share wani dakin daban.

Alkali Michael Obus ya shaida wa kotun cewa: "na fahimci cewa yanayin wannan shari'a ya sauya matuka gaya, don haka na amince cewa hadarin [Mista Strauss-Kahn] zai gudu ya ragu sosai. Saboda haka na saki Mista Strauss-Kahn a bisa sharadin yarda da shi."

Sai dai alkalin ya kara da cewa babu bukatar gaggawa wajen yanke hukunci.

A kofar kotun kuwa, lauyoyin bangarorin biyu jaddada matsayinsu suka yi.

"Ina son tuna muku gaba daya cewa duk zuwan da muka yi kotu a makwanni shidan da suka gabata, mun neme ku da kada ku yi gaggawar yanke hukunci--ina ganin yanzu za ku fahimci dalilin da ya sa", in ji lauyan Mista Strauss-Kahn, William Taylor.

Ya kuma kara da cewa, "Mun yi amanna cewa mataki na gaba zai kai ga watsi da karar".

Bayan zaman kotun na ranar Juma'a dai, Mista Strauss-Kahn ya fito yana murmushi rike da kafadar matarsa.

A zaman da kotun ta yi a baya dai masu shigar da kara sun ce suna da kwakkwarar hujja.

Lauyan matar da ke zargin Mista Strauss-Kahn, Kenneth P. Thompson, ya jaddada cewa wacce ya ke karewa ta yi sahihin bayani kuma Mista Strauss-Kahn ya aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa.

"Hujjar da Mista Strauss-Kahn ya ke kare kansa da ita daya ce tak: cewa sun sadu ne da amincewar juna; wannan karya ce", in ji shi.

Ya kuma yi dogon jawabi, wanda a ciki ya zayyana duk abin da ya wakana tsakanin ma'aikaciyar otal din da Mista Strauss-Kahn, sannan kuma ya yi kakkausar suka a kan Lauyan Gwamnati Cyrus Vance.

Ranar 18 ga watan Yuli Mista Strauss-Kahn zai sake bayyana a gaban kotu.

Ma'aikaciyar otal din dai ta yi zargin cewa Mista Strauss ya bi ta da gudu har falon dakinsa na otal din Sofitel mai tsadar gaske, sannan ya yi yunkurin tube mata wando da kuma tilasta ta yin jima'i da shi.

Sai dai jami'an tsaro sun bayyanawa kafofin yada labarai na Amurka cewa matar ta yi ta karerayi tun bayan yunkurin da ta ke zargin ya yi mata fyade ranar 14 ga watan Mayu.

Jami'an sun ce sun yi amanna matar ta yi karya a takardunta na neman mafaka a Amurka, musamman ma zargin da ta yi cewa an yi mata fyade a kasarta ta haihuwa, wato Guinea.

Wani jami'in tsaro ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa: "Tabbas ta fedewa masu shigar da kara biri har bindinsa, amma daga bisani sai ta ce karya ce".

To amma ranar Juma'a Mista Thompson ya kare matar, tare da zayyana abin da ya faru tsakaninta da Mista Strauss-Kahn.

"Tun daga ranar farko ta zayyana yadda Mista Strauss-Kahn ya yi yunkurin keta mutuncinta", in ji Mista Thompson, wanda ya kara da cewa Mista Strauss-Kahn ya kayar da matar a kasa har sai da ta kuje.

"Ba ta taba sauya ko da kalma daya a bayanin nata ba; shi lauyan gwamnati ya san haka", in ji Mista Thompson.

Mista Thompson ya kuma ce ko da ma'aikaciyar otal din ta yi kurakurai, hakan ba zai sa a ce ba a yi mata fyade ba.

Wannan juyin wainar da aka samu a shari'ar dai ya farfado da fatan wadansu mutane na ganin Mista Strauss-kahn ya yi takara da Nicolas Sarkozy a zaben shugaban kasar Faransa a shekarar 2012.

Karin bayani