Shugaban Venezuela na fama da ciwon daji

Chavez na fama da ciwon daji Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Hugo Chavez

Shugaba Hugo Chavez na Venezuela ya ce an yi masa aikin fida sakamakon ciwon dajin da ya ke fama da shi.

A wani jawabi da ya yi daga Cuba, inda ya ke jinya a wani asibiti, Shugaba Chavez ya ce da farko likitoci sun yi masa fida don warkar da wani kumburi da ke kugunsa.

Ya ce daga bisani likitocin sun gano wani kumburin da ke dauke da kwayoyin cutar daji a jikinsa, abin da ya sanya aka gudanar da wata sabuwar tiyatar.

Shugaban dai ya rame sosai, kuma yana jawabin ne cikin murya mai sanyi.

Jawabin na Shugaba Chavez ya tabbatar da hasashen da aka yi ta yi a Venezuela cewa girman rashin lafiyarsa ya wuce yadda aka kimanta tun farko.