Shugaban China ya gargadi 'yan jam'iyar Kwaminis

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hu Jintao

Shugaban China, Hu Jintao, ya gargadi 'yan Jam'iyyar Kwaminis mai mulkin kasa kan su guji cin hanci idan ba haka ba jam'iyyar za ta rasa goyon baya, da amincin da ta ke samu daga wajen 'yan kasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a ranar jajiberen bukukuwan cika shekaru casa'in da kafa jam'iyyar.

Mista Hu ya kuma gargadi 'yan jam'iyyar su guji yin amfani da mulki wajen amfanar da wasu mutane 'yan tsiraru.

A gefe guda kuma, kasar China ta amince da wata sabuwar doka wadda za ta sanya da wuya gwamnati ta iya fitar da mutane daga gidajensu da karfi.

Kafofin yada labaran Chinan sun ce wannan doka ce da a tarihin tsarin shari'a na kasar aka jima ana sauraronta.