Ana shakku kan kimar matar da ta zargi Strauss Kahn

Dominique Strauss Kahn Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dominique Strauss Kahn

An samu sabbin alamun tambaya akan zargin yunkurin yin lalata da wata ma'aikaciwar otel, da akeyi wa tsohon shugaban hukumar bada lamuni ta duniya - IMF.

Wasu masu bincike sun shaidawa wata jaridar Amurka cewa da wuya ayi aiki da duk wani abunda maikaicyar otel din ta fada saboda an alakanta ta, da wani dillalin miyagun kwayoyi da aka taba daurewa.

Rohotanni sunce an nadi muryar matar tana tattaunawa da tsohon dillalin kwayoyin a kan irin abunda za'a samu idan aka ci gaba da shara'ar.

Wata mata a Paris ta bayyana cewar tun farko ta na da shakku game da zargin.

Ta ce,"ai dama na san cewa sharri ne.Kuma matar na yi ne don ta samu kudi.

mutumin yana burge ni sosai, kuma ban taba yadda da zargin ba".