Kwamitin Lemu ya zauna a Bauchi

Kwaminitn da gwamnatin tarrayar Najeriya ta kafa domin binciken rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar, Dakta Goodluck Jonthan, a watan Afirilu a wasu jihohi na Najeriya na ci gaba da gudanar da aikinsa inda ya ziyarci jihar Bauchi, wato daya daga cikin jihohin da aka samu tashin hankalin. Daruruwan mutane ne dai suka rasa rayukansu a tashin hankalin na bayan zabe yayin da wasu suka jikkata baya kuma ga hasarar dukiya. A jihar ta Bauchi dai kwamitin ya yi wani zaman sauraren ba'asi daga jama'a kan tashin hankalin wanda yan siyasa ke dora wa junansu laifin haddasawa.

To sai dai kuma wasu da lamarin ya shafa ba su samu damar gabatar da ba'asinsu a lokacin da suka ziyarci wurin zaman kwamitin ba.