'Yan kwadago za su tafi yajin-aiki a Najeriya

Image caption Taswirar Najeriya

Gamayyar Kungiyoyin Kwadagon Najeriya karkashin kungiyar kwadago ta kasa ta sha-alwashin fara yajin-aiki idan gwamnati ta gaza biyan albashin da ta yi alkawarin baiwa ma'aikata.

Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin kasar sun amince su rika biyan Naira dubu goma sha takwas a matsayin albashi mafi karanci.

Sai dai a makon jiya, gwamnatocin jihohin sun ce ba za su iya biyan albashin ba sai sun samu karin kudi daga asusun Tarayya.

Amma a martanin da suka mayar kan batun, kungiyoyin kwadagon sun baiwa gwamnatocin wa'adin makonni biyu su aiwatar da sabon albashi ko 'yan kwadagon su shiga yajin-aiki.

Shugaban kungiyar Abdulwahid Omar ne ya bayyana hakan a wani taro da kungiyar ta gudanar ranar Alhamis a Abuja.