Ra'ayi Riga: Matsalar ambaliyar ruwa

Ambaliyar ruwa a Kano
Image caption Jama'a sun rasa rayukansu a ambaliyar ruwan da akai a Fagge, Kano

A cikin kwanakin da suka gabata ne hukumomin lura da yanayi da kuma hasashe na kasashen Nijeriya da Nijer suka bayyana cewa suna hasashen cewa za a tafka ruwan sama a bana, abinda kuma zai iya jawo ambaliyar ruwa, da asarar dukiyoyi da ma kuma rayuka.

Jim kadan bayan wannan hasashe sai kuwa ga shi an tafka wani ruwan sama wanda ya janyo ambaliyar ruwa a Unguwar Fagge dake Kano a Nijeriya.

A taikaice har yanzu al'umomi da dama a jihohin Jigawa da Sakkwato da kuma sassa daban daban na jamhuriyar Nijar kamar Agadez da Maradi da Yamai ba su gama farfadowa ba daga ambaliyar ruwan da aka samu a bara.

Gwamnatoci dai kan yi alkawarin daukar matakai domin magance samun asarar rayuka ko dukiyoyi idan har an sami irin wannan ambaliyar ruwa.

Ganin cewa damina ta fara nisa, shin wadanne matakai hukumomi suke dauka domin kaucewa afkuwar irin matsalolin da aka samu a bara, wacce gudunmawa su kansu jama'a zasu bayar domin kaucewa shiga hadari. Wadannan su ne irin batutuwan da zamu tattauna a shirin na yau.

Tare da ni kuma yanzu haka akwai:

Malam Nuhu Alhassan, mataimakin darakta kan tsare-tsare da bincike da kuma hasashe na hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya Nema,

da Alhaji Abdullahi Abbas, kwamishinan muhalli na jihar Kano.

da Malam Salisu Auwal babban jami'i a hukumar hasashen yanayi ta Nijeriya,

a Jamhuriyar Nijer kuma muna tare da wakilinmu a Yamai, Iddy Baraou.