Dubban masu zanga zanga sun fantsama kan tituna a Syria

Dubban mutane sun fantsama kan tituna a garuruwa daban daban a kasar Syria, domin gudanar da zanga zangar nuna kin jinin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

'Yan adawa sun ce akalla mutane miliyan uku ne suka shiga cikin zanga zangar da ake ganin na cikin mafi girma da ake tayi a kasar ta Syria, ko daya ke ba'a tabbatar da adadin ba.

Zanga zangar dai ta fi kamari a garin Hama, dake arewacin birnin Damascus.

Masu fafutuka sun ce jami'an tsario sun harbe har lahiya akalla masuzanga zangar goma a duk fadin kasar.