Isa Yuguda ya nemi gafara daga 'yan Boko Haram

Muhammad Yusuf, shugaban kungiyar da aka kashe
Image caption Muhammad Yusuf, shugaban kungiyar da aka kashe

Rahotanni daga Nijeriya na cewa Gwmnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya nemi gafarar kungiyar nan ta Jama'atu Ahlul Sunnah Walidda'ati waljihad da aka fi sani da Boko Haram wadda ke daukar alhakin kai hare-haren bama-bamai da na bindiga a wasu jihohi na kasar.

Shi dai gwamnan na jiohar Bauchi Malam Isa Yuguda, ya nemi gafara daga yayan kungiyar ta jama'atu Ahlul Sunnah Lidda'awati Wl Jihda ne a wata sanarawar da ya bada ga manema labarai inda ya ce su yafe masa duk wani rashin jin dadi ko kuma kunci da ta yiwu ya haddasa masu.

Jihar ta Buchi dai na daya daga cikin jihoihin da aka fi samun tashe-tashen hankulan da ake dangantawa da kungiyar ta Boko Haram.