Ana sake shata iyakokin Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Hukumar Shata Iyakoki ta Nijeriya na gudanar da aikin sake shata iyakokin wasu jihohi a kasar.

Babban Daraktan Hukumar, Dakta Muhammad Bose Ahmad, ya shaidawa BBC cewa ana yin hakan ne sakamakon yawan tashe- tashen hankula da ake samu tsakanin al'umomin da ke kan iyakokin wasu jihohi.

Ya ce shata iyakokin zai magance rikice-rikicen da kan kai ga asarar rayuka da dukiya. Yanzu haka dai hukumar tana kokarin gudanar da wannan aiki a iyakokin jihar Bauchi, da jihohin Jigawa, da Taraba inda ake da matsaloli.