'Yan tawayen Libya sun yi maraba da tayin Tarayyar Afrika

Shugaba Ghaddafi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Ghaddafi

Majalisar wucin gadi ta 'yan tawayen Libya ta shaidawa BBC cewa ta yi maraba da tayin da tarayyar Afrika ta yi na yin tattaunawa ba tare da shugaba Ghaddafi ba.

Majalisar ta ce wannan zai bayar da damar shirye-shiryen wucin gadi ba tare da shugaban ba.