Libya za ta kai hari akan kasashen Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu goyon bayan Gaddafi

Shugaban Libya, Mu'ammar Gaddafi, ya yi barazanar fara kai hari akan kasashen Turai, idan kungiyar NATO ba ta dakatar da hare-haren da take kaiwa a Libya ba.

Shugaba Gaddafi ya ce 'yan kasar Libya za su fantsama cikin kasashen Turai, su kai hari a gidaje da kuma ofisoshi.

Kanar Gaddafi ya ce: '' Zamu iya keta haddin gidajenku, da ofisoshinku, da kuma iyalanku, domin kuwa dukkansu za su iya zama wuraren da za a iya kaiwa hari kamar yadda dakarun NATO ke yi a Libya''.

Shugaba Gaddafi ya yi jawabin ne a wani faifai da aka nada, wanda mabiyansa suka saurara.

A bangare guda kuma, wasu kungiyoyin kare hakkin Bil Adama a jamhuriyar Nijar sun yi tur da hare-haren da ake kaiwa Libya.

Kungiyoyin sun ce ana kai hare-haren ne da zummar sake yi wa kasashen Afrika wani sabon mulkin mallaka.