Za a tattauna tsakanin gwamnati da 'yan adawa a Bahrain

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sarki Hamad

A yau Asabar ne za a fara tattaunawa tsakanin gwamntin Bahrain da kuma 'yan adawar kasar.

Sarkin kasar, Sarki Hamad, wanda mabiyin tafarkin Sunni ne, ya ce za a kokarin yin sulhu yayin tattaunawar da babban bangaren 'yan adawa na mabiya tafarkin Shi'a zai laharta.

Wannan tattaunawa dai na zuwa ne bayan an kashe mutane talatin a watannin da aka shafe ana zanga-zangar nuna kin- jinin gwamnati.

Har yanzu dai ana cigaba da tsare da daruruwan magoya bayan 'yan adawar kasar ta Bahrain a gidajen yari.