Tarayyar Afirka ta yi watsi da umarnin Kotun Duniya kan Libya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Jean Ping

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi kira ga mambobinta kada su aiwatar da umarnin da Kotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya ta bayar na kama shugaban Libya, Mu'ammar Gaddafi.

A karshen taron da suka yi a Equitorial Guinea, shugabannin kasashen Afirkan sun ce umarnin kama Gaddafi da kotun ta bayar ya kawo tarnaki ga kokarinsu na kawo karshen rikicin na Libya.

Sun ce Kotun ba ta yiwa shugabannin nahiyar adalci kasancewa su kadai ta ke ba da umarnin kamawa.

Shugabannin sun bayyana Babban Mai Shigar da Kara na Kotun, Lius Moreno Ocampo da cewa mutum ne maras alkibla.