Mutane da dama sun mutu a Maiduguri

'Yan sanda na bincike a Nijeriya
Image caption 'Yan sanda na bincike a Nijeriya

Bama-bamai sun kashe mutane da dama a wata mashaya a birnin Maiduguri da ke Arewacin Najeriya, sa'o'i kadan bayan wasu 'yan bindiga sun harbe Shugaban Riko na Karamar Hukumar Jere, Alhaji Mustapha Baale har lahira.

Jami'an tsaro sun tabbatarwa da BBC cewa mutanen sun mutu ne sakamakon harin da ake zargin 'yan bindiga da kaiwa a mashayar, sai dai ba su tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba.

Gabanin aukuwar lamarin, 'yan bindigar sun harbe Alhaji Mustapha Baale a unguwar Old Maiduguri da ke yankin Karamar Hukumar Jere.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan harbe wasu mutane da tsakar daren ranar Lahadi a unguwar Bulabulin Ngarman da ke tsakiyar birnin, inda kimanin mutane hudu suka mutu.