Chavez ya koma Venezuela bayan jinya a Cuba

Shugaba Hugo Chavez Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Shugaba Hugo Chavez

Shugaba Hugo Chavez ya koma gida Venezuela daga kasar Cuba, inda ya ce an yi masa aikin tiyatar ciwon daji ko kansa.

Mr Chavez ya bayyana cewar yana jin jikinsa garau, kuma yana farincikin komawa gida, a daidai lokacin bikin samun 'yancin kan kasar ta Venezuela.

Hugo Chavez ya kwashe kusan wata guda a Cuba, inda likitoci suka cire masa wani karin cutar dajin.

Dadewar da yayi a Cubar, da kuma boye boyen da aka yi da farko game da yanayin lafiyar tasa, sun haddasa rashin tabbas da kuma cece- kuce a Venezuela, kasar da ya kwashe tsawon shekaru 12 yana shugabanta.