Tarayyar Turai za ta baiwa Koriya Ta Arewa tallafi

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Tutar Tarayyar Turai

Kungiyar Tarayyar Turai za ta aike da tallafin gaggawa na abinci na kimanin dala miliyan goma sha biyar zuwa Korea Ta Arewa.

Kungiyar ta EU ta ce, fiye da mutane dubu dari biyar na iya rasa rayukansu sakamakon rashin abinci mai gina jiki a kasar.

Kungiyar ta kara da cewa Korea ta Arewa ta amincewa cewa jami'anta su sanya ido akan yadda za a raba tallafin abincin ga mabukata.

Wata tawagar gani-da-ido ta kungiyar ta EU da ta je Korea ta Arewan a watan da ya gabata ta ce, karancin abinci ya munana fiye da bara, inda a yanzu wasu suke cin ciyawa domin su rayu.