Shugaba Chavez ya yi jawabi ga magoya bayansa

Hugo Chavez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An ta rade-radi a kan lafiyar shugaba Chavez

Shugaba Hugo Chavez na kasar Venezeula ya gabatar da jawabi a gaban dubun dubatar magoya bayansa a cikin harabar fadar shugaban kasa a Caracas babban birnin kasar, bayan daya dawo daga kasar Cuba.

Tare da 'yayansa mata a kusa da shi, Mr Chavez ya rika daga tutar Venezuela kuma ya jagoranci magoya bayansa wurin rera taken kasar.

Daga nan kuma ya gabatar da jawabi a tsaye kuma ba tare da ya rike wata takardaba na tsawon mintocci talatin.

Ya mika godiyarsa ga magoya bayansa da suka nuna masa kauna kuma ya lashin takobin ganin ya samu koshin lafiya.

Sai dai ya ce wanan abu ne dake bukatar a bishi daki -daki kamar yadda wani shiri me tsauri da likitocinsa suka tsara masa ya shinfada.

Mr Chavez ya shafe makonni uku ana jinyarsa a birnin Havana, inda akayi masa aikin tiyata akan cutar sankara ko cancer .

Sai dai duk da cewa Mr Chavez ya dawo a dai dai lokacin da kasar ke bikin cika shekaru dari biyu da kafuwa amma ya ce ba zai samu damar halatar bikin ba.