Sabuwar shugabar IMF za ta fara aiki

Christine Lagarde Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Christine Lagarde ce mace ta farko da aka taba zaba a mukamin

Tsohuwar ministar kudi ta Faransa Christine Lagarde zata kama aiki a matsayin shugabar asusun bada lamuni ta duniya wato IMF a yau.

Ita ce mace ta farko da zata shugabanci hukumar, kuma an nada tane bayan an kama Dominique Strauss Kahn bisa zargin aikata fyade a cikin watan Mayu.a.

Dukkanin shugabanni goma da suka taba rike wanaan mukami, kafin ita daga turai suka fito kuma ita ce yar kasar faransa ta biyar da za'a ba wanan mukami.

Sai dai tarayar turai ita ce zata tabbatar da yadda kamun ludayinta zai kasance yayinda shine babban kalubalen dake gabanta.

Wuri na farko zata fi baiwa fifiko ba tare da bata lokaci ba, shine matsalar bashin da yankin Turai ke fuskanta.

Ana dai bukatar a dauki mataki nan da wasu kwanaki masu zuwa akan ko asusun bada lamuni, zai ba Girka talafin ceto tattalin arzikin kasar zagaye na biyu.