Majalisar wakilai za ta ci gaba da daidaita rabon mukamai

Zauren majalisar Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A baya an samu cikas wajen rabon mukaman

A Najeriya, a yau ne ake sa-ran Majalisar wakilan kasar za ta ci gaba da daidaita rabon mukamai na manyan jami'ai a tsakanin`yan majalisar.

Sai dai rahotanni na nuna cewa watakila matakin da`yan majalisar za su dauka zai saba da umurnin da iyayen jam`iyyunsu suka ba su.

Jam`iyyar PDP da takwararta ta CPC dai sun nuna inda fuskokinsu suka karkata danganeda wannan rabon, amma alamu na nuna cewa`yan majalisar za su juya musu baya.

Rahotanni sun ce jam'iyyar CPC na yunkurin ganin 'yayanta sun zabi me tsawartawa na marasa rinjaye a majalisar wakilan da ya fito daga shiyyar Arewa ta tsakiya, sai dai akasarin 'yayanata sun ce 'dan shiyyar Arewa maso yammacin kasar ne zasu zaba.

Su kuwa 'yayan jam'iyyar PDP a majalisar sun ce duk da cewa sun amince shugaban masu rinjaye ya kasance 'dan shiyyar kudu maso yammacin kasar amma su zasu zabi mutumin da suke so.