'Ma'aikatan Najeriya zasu gani a kasa nan ba da jimawa ba'

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Sabon ministan kwadagon Najeriya, Emeka Wogu, ya ce nan da mako guda zai warware takaddamar dake tsakanin kungiyar kwadagon kasar da gwamnati.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin wata ziyarar da ya kai ofishin kungiyar kwadagon dake Abuja.

A makon jiya ne dai kungiyar kwadagon ta bada wa'adin makonni biyu ga gwmanatin Najeriyar, na ta aiwatar da sabon tsarin albashi mafi kankanta na Naira dubu 18 - idan ba haka ba kwa ta shiga yajin aiki.