Za a kafa gwamnatin hadin gwiwa a Thailand

Yingluck Shinawatra Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yingluck Shinawatra za ta zamo Fira Ministan Thailand

Jam'iyyar Pheu Thai wacce ta samu nasara a zaben kasa baki dayan da aka gudanar a kasar Thailand, ta ce za ta kafa gwamantin hadin gwiwa da wasu kananan jam'iyyu hudu.

Jam'iyyar, karkashin jagorancin Yingluck Shinawatra, 'yar uwar tsohon Fira Minista Thaksin Shinawatra - ta lashe zaben da kujeru 265.

Fira Minista Abhisit Vejjajiva ya bada sanarwar yin murabis daga shugabancin jam'iyyar Democrats, wacce ta lashe kujeru 160.

Rundunar sojin kasar wacce ke da karfin gaske, ta ce za ta amince da sakamakon zaben na ranar Lahadi.

Ms Yingluck, wacce ba ta da wata gogewa ta siyasa a baya, ta ce Pheu Thai da wasu jam'iyyu hudu "sun amince su yi aiki tare domin shawo kan matsalolin kasar".

"Babban lamarin shi ne yadda za a kai ga sasanta wa," a cewarta.

Sojoji ne suka yi wa Mr Thaksin juyin mulki a shekara ta 2006, kuma masu adawa da 'yar uwarta sa sun ce 'yar amshin shatarsa ce kawai.

Amma da yake magana daga Dubai inda yake tilastawa kansa zaman gudun hijira, Mr Thaksin ya ce ba ya son komawa fagen siyasar Thailand.

Karin bayani