Bom ya kashe soji a Maiduguri

Image caption Jami'an tsaro na daga cikin wadanda hare-haren suka fi ritsawa da su

Rahotanni sun bayyana cewa wani bom da ya tashi a garin Maiduguri ya yiwa rundunar sojin Najeriya Mummunar barna, inda aka ce an samu hasarar rayuka.

Wata majiyar asibiti ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an kai gawarwakin soji hudu mutuware.

Amma wata majiya a rundunar sojin ta ce sojoji uku ne suka samu rauni a harin wanda aka kai a shingen sintirinsu a unguwar Abbaganaram da ke tsakiyar garin na Maiduguri.

Tunda farko an ji karar An ji karar fashewar wani abu tare da harbe-harben bindiga a garin Maiduguri da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, inda kungiyar Boko Haram ta saba kai farmaki.

Wakliyar BBC Bilkisu Babangida a Maiduguri, ta ce fashewar ta afku ne da misalin karfe 7 na safe, sannan kuma aka ji karar harbe-harben bindiga.

"Jama'a sun fita a guje domin ganin inda abin ya fashe. Daga nan kuma sai hayaki ya turnuke sararin samaniyar unguwar ta Abbaganaram," kamar yadda wani da ya shaida abin ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Sojoji sun datse hanyoyin da ke kaiwa ga tsakiyar Birnin, abin da ya sanya ma'aikatan da suka fito aiki komawa gida.

A jihar Bauchi ma....

Hakazalika rahotanni daga jihar Bauchi a Arewa maso Gabashin Najeriyar na cewa an ji karar harbe-harbe a garin Toro a daren ranar Laraba.

Rahotanni sun ce 'yan bindiga ne suka kai hari wani ofishin 'yan sanda inda suka yi a wangaba da bindigogi da alburusai da dama.

Mazauna garin dai sun shaida wa BBC cewa karar harbe-harben a wajejen caji ofis na 'yan sanda da kuma wani banki, ta jefa su cikin fargaba.

Image caption Wata mashaya da 'yan Boko Haram suka bankawa wuta

Babu dai tabbacin hasarar rayuka ko kuma jikkata ko ma manufar masu harbe-harben, kuma kokarin BBC domin jin ta bakin hukumomin tsaro ya ci tura.

To sai dai wani jami'in karamar hukumar Toro ya tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya zo bayan sa'o'i da jami'an tsaro suka yi musayar wuta da 'yan bindiga a cikin garin Bauchi.

Ita ma dai jihar ta Bauchi na fama da matsalar 'ya'yan kungiyar Boko Haram, wacce ke fafutukar kafa tsarin shari'ar musulunci a Arewacin Najeriyar.

A 'yan kwanakin nan kungiyar ta zafafa hare-haren da ta ke kaiwa musamman a yankin Arewa maso Gabashin kasar. A kalla mutane 150 ne ake tunanin sun mutu tun daga watan Janairun bana.

Sai dai kungiyar ta kai wasu hare-haren ma a wajen Maiduguri, ciki harda harin bom a hedkwatar 'yan sandan kasar da ke Abuja a watan da ya gabata.

A ranar Litinin Hukumar 'yan sanda ta farin kaya a Najeriya (SSS), ta ce ta kama mutane 100 da ta ke zargin 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram ne sannan ta bankado wani yunkuri dana bam kimanin wata daya da rabi da ya wuce.

Duka shugaba Jonathan da kuma gwamanan jihar Borno Kashim Shatima sun yi tayin afuwa ga kungiyar domin a fara tattaunawa kan yadda za a shawo kan matsalar, amma kungiyar ta yi watsi da bukatar ta su.