An kashe jami'an tsaro akalla hudu a Maiduguri

Muhammad Yusuf
Image caption Madu Shariff ya nemi ahuwar 'yan Boko Haram

Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno na cewa an harbe jami'an tsaro akalla hudu, daga wayewar garin yau, zuwa yammaci a hare haren da yan bindiga suka kai a karo daban daban.

Hukumomin tsaro a jihar ta Borno sun tabbatar da aukuwar lamarin, suna kuma zargin 'yan kungiyar nan ta Jama'atu Ahlil Sunna Lidda'awati wal jihad ne, da aka fi sani da suna, Boko Haram, da kai hare haren.

Kungiyar dai ta sha ikirarin kai hare hare na bindiga da bamabamai a sassa daban daban na wasu jihohin arewacin Nijeriya har da Abuja.

A batun kuma, tsohon Gwamnan jihar Bornon, Madu Shariff, ya nemi ahuwar 'yan kungiyar ta Boko Haram a kan duk wani laifi da ya yi masu a baya.

To can ma a Jihar Bauchi wasu rahotannin na cewa jami'an tsaro sun yi musayar wuta da wasu 'yan bindga a garin Bauchin, inda wasu bayanai ke cewa an sami hasarar rayuka.

Rundunar 'yansandan jihar Bauchin dai ta bayyana cewa ta kai samame ne a maboyar yan bindigar domin ta samu bayanan sirri dake cewa mutanen na dauke da makamai.

Koda yake dai rundunar yansandan ba ta yi wani Karin bayani ba dangane da ko su wanene yan bindigar ba, to amma unguwar da lamarin ya faru wurin ne da wasu ke yi ma kallon matattara ta 'yan kungiyar nan na Boko Haram.