ECOWAS na taro a kan matsalar rashin muhalli

A Najeriya, yau ne ake wani taron ministocin muhalli daga kasashen kungiyar raya tattalin arzikin yankin Afirka ta Yamma, ECOWAS/ CEDEAO.

Taron wanda aka bude dazu a Abuja na nufin tattaunawa a kan hakkokin wadanda wasu dalilai suka raba da gidajensu.

A Nigeria akwai mutane da dama suka rasa muhallansu sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar na watan Afrilun da ya gabata.

Ana saran taron zai haifar da wani kudurin tarayyar Afirka a kan ba da kariya ga wadanda wasu dalilai suka raba da gidajensu a nahiyar, wanda aka fi sani da Yarjejeniyar Kampala.