'Yan tawayen Libya sun yi ikirarin nasara

'Yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Har yanzu ana fama kiki-kaka

‘Yan tawayen Libya sun ce sun samu nasarar kafa wata dangar tsaro a kudu da kuma yammacin birnin Misrata, ta hanyar hade fagagen fama guda biyu.

Haka kuma sun nuna wa BBC sojoji da yawa daga dakarun Kanar Gaddafi da aka jikkata , aka kuma kama a lokacin fada.

Ana dai ta artabu a kusa da Misrata tun da sanyin safiya zuwa rana.

Haka kuma an yi bata -kashi a zagayen Brega a gabaci da kuma a tsaunukan Nafisa a kan iyakar Tunisia, to amma wakilin BBC a Misrata ya ce babu wani bangare da ke samun wani muhimmin ci gaba.