Babban bankin Nijeriya zai bunkasa noma

Babban bankin Nigeria CBN, ya bullo da wani sabon shiri na inganta harkokin noma da kiwo a kasar.

Sabon shirin, wanda ya hada hukumomin ma'aikatun noma da kudi, da dukan bankunan Najeriyar, da kuma manoman su kansu, zai bude wani sabon babi na sarrafa kayayyakin amfanin gona da ake nomawa a kasar.

Makasudin yin hakan shine, manoma su rika cin ribar abinda suke nomawa.

Harkar noma dai ita ce ke samar da kusan kashi sittin cikin dari, na guraben aikin yi a Nigeria.

Sai dai rashin bai wa noman muhimmancin gaske daga bangaren gwamnati da kuma majalisar dokoki, na yi wa aiyukan noman tarnaki.