An kashe mutane kimanin 80 a Afghanistan

Mummunan ba-ta-kashi tsakanin 'yan kungiyar Taleban da jami'an tsaron Afghanistan a gabashin kasar, ta kai ga mutuwar 'yan sandan kan iyaka guda talatin da ukku, da fararen hula biyar, da kuma masu fafitikar guda arba'in.

Gwamnan lardin Nuristan, Jamaluddin Badar, ya sheda wa BBC cewa an fara fadan ne ranar Litinin da dare, aka kuma kwashe kwanaki biyu ana yi.

Dakarun masu fafitika fiye da dari da hamsin ne da ke dauke da jibgin makamai, suka ketara, suka shiga kasar daga gundumar Chitral a Pakistan, suka shiga lardunan Nuristan da na Kunar a Afghanistan din.