Tuhumar da ake yiwa Domique Strauss Kahn

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mr Dominique Strauss Kahn

Alkalin wata kotu a New York dake Amurka wanda kuma ke jagorantar karar da ake yiwa tsohon shugaban hukumar bada lamuni na duniya wato IMF Dominique Strauss Kahn, akan zarge zargen aikata fyade, yaki amincewa da wani kiran da akayi masa na ya sauka.

Lauyoyin dake kare matar dake zargin Mr Strauss Khan da aikata fyade ne dai sun ce Alkalin Cyrus Vance, ya yiwa karar tasu zagwon-kasa, ta hanyar tona asirin wasu bayanai game da matar.

Sai dai Ofishin Mr Vance yace bukatar tasu ba tada makama.

Daga bisani lauyoyin Mr Kahn da kuma masu shigar da kara sun tattauna cikin sirri na tsawon mintocci casa'in a wani yunkurin ganin ko za'a iya sansanta bangarorin biyu.