Mutane Saba'in sun hallaka a India

Image caption Wani hadarin jirgin kasa a India

Hadarin ya auku ne a cikin wani karamin gari a yammacin Uttar Pradesh me nisan kilomita 300 da gabashin Delhi babban birnin kasar India.

Motar bus din na kan hanyar dawowa daga wata liyafar bikin daurin aure da misalin karfe biyu na safiya a lokacin da jirgin kasan ya afka masu.

Wani dan jarida a kasar ya ce jirgin kasan ya rika 'jan bus din me dauke da fasinjoji masu yawa akan titi.

Mutane dake zaune a saman bus din sun fado kasa kuma sun samu munanan raunuka yayinda wandanda ke ciki suka hallaka.

Da dama daga cikin wadanda suka samu raunuka na kwance a wani asibiti inda ake jinyasu yayinda ake cigaba da kokarin ceto mutanen da suka makale a cikin motar.

Daya daga cikin mutanen da suka sami raunuka ya shaidawa wani dan jarida cewa yana zaune ne a saman bus din a lokacin da ya hango jirgin kasa na tahowa kusa da kusa da su.

Ya ce ya gargadi matukin bus din amma be nuna alamun ya saurare shi ba.