Ali Modu Sheriff ya nemi afuwar Boko Haram

Ali Modu Sheriff Hakkin mallakar hoto google
Image caption Ali Modu Sheriff ne gwamnan Borno daga 2003 zuwa 2011

Tsohon gwamnan jihar Borno a Najeriya Ali Modu Sharif, ya nemi afuwa ga 'ya'yan kungiyar Boko haram wacce ke kai hare-hare mafi yawanci a garin na Maiduguri.

A lokacinsa ne dai aka kashe shugaban kungiyar Muhammad Yusuf bayan da jami'an tsaro suka kamashi.

Abin da kuma ana ganin shi ne ya kara harzuka 'ya'yan kungiyar.

"Ina so na mika bukatar neman afuwa ga kungiyar Jama'atu Ahliss-Sunnah lidda'awati wai jihad...Mai yi wuwa na muzguna musu a lokacin da na ke gwamnan jihar Borno," kamar yadda Modu Shariff ya fada a wata sanarwa da ya wallafa a wata jaridar kasar.

An zargi Sheriff, wanda ya shugabanci Borno daga 2003 zuwa 2011, da laifin hannu a murkushewar da jami'an tsaro suka yi wa Boko Haram, lokacin boren da kungiyar ta yi a 2009.

"Duka dan adam na yin kuskure, yayin da Allah ke yin gafara," a cewar tsohon gwamnan.

An ji fashewar wani abu

Wannan ita ce afuwa ta uku a jere da ta fito daga bakin manyan 'yan siyasa daga Arewacin Najeriya a cikin mako guda.

A makon da ya gabata, tsohon gwamnan jihar Gombe Sanata Danjuma Goje da na makwafciyar jihar Bauchi Isa Yuguda, a sanarwar da suka bayar daban daban, sun nemi afuwa ga kungiyar ta Boko Haram kan duk wata rawa da suka taka a lokacin boren na 2009.

An kuma wayi gari da jin karar fashewar wani abu tare da harbe-harben bindiga a garin na Maiduguri.

Wakiliyar BBC ta ce fashewar abun da ake kyautata zaton cewa bam ne, ya auku ne a wata unguwa a tsakiyar birnin.

Kungiyar ta Boko Haram ta fi karfi a Borno, amma tana da magoya baya a wasu jihohin Arewacin kasar.

Karin bayani