Ana zargin gwamnan Zamfara da yin facaka

A jihar Zamfara dake arewacin Najeriya, babbar Jam'iyyar adawa ta PDP a jahar ta zargi sabon gwamnan jahar da abin da ta kira, yin facaka da kudaden gwamnati.

Jami'yyar na zarginsa da shatar jirgin sama domin yin tafiye- tafiye zuwa wasu sassan kasar, maimakon amfani da motar da aka tanadar masa.

Ta ce hakan be dace ba saboda gwamnatin sabuwa ce amma ta fara nuna alamun bin wasu hanyoyi na barnar kudi.

Sai dai Gwamnan na jam'iyyar ANPP ya musanta hakan, inda yace gwamnatin jam'iyyar PDPn daya gada, bata bar masa ko taro ba a cikin asusun jahar, da har zai yi facaka dasu.