Al-Bashir zai halarci bikin 'yancin Sudan ta Kudu

Shugaba Usman Hassan al-Bashir Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Akwai babban kalubale a gaban Shugaba al-Bashir

Shugaba Usman Hassan al-Bashir ya ce zai je Kudancin Sudan domin halartar bikin samun 'yancin kan kasar ranar Asabar.

Ya kuma ce zai nemi dangantaka mai kyau da sabuwar kasar wacce yakin basasa ya daidaita.

"Zan yi tattaki zuwa babban birnin Kudancin Sudan (Juba) nan da kwanaki biyu masu zuwa domin taya su murna kan 'yancin da suka samu.

"Zan kuma yi musu fatan zaman lafiya da samun alkhairi," a cewar Bashir, yana magana a wurin bikin bude wata gada.

Kudancin Sudan mai arziki mai zai samu 'yancin kai a hukumance ranar Asabar - biyo bayan kuri'ar raba-gardamar da aka yi a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a shekara ta 2005.