Masu bore a Masar na dawowa dandalin Tahrir

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga zanga a Masar

Kusan watanni shida tun bayan hanbarar da shugaban kasar Masar Hosni Mubarak daga kan mulki, masu bore a kasar na dawowa zuwa tsakiyar birnin Alkahira, gabanin shirye- shiryen da suke na gudanar da wata zanga- zangar nuna rashin gamsuwa game da yadda ake samun tafiyar hawainiya a kasar.

Waiklin BBC yace masu zanga- zangar na kafa tantina a dandalin Tahrir, sune kuma ke baiwa motoci hannu a tsakiyar babban birnin kasar, inda jami'an 'yan sanda suka kauracewa yankin domin gudun yin fito na fito.

Kungiyoyin 'yan adawa ne dai suka kira zanga zangar, wadanda ke korafin cewar ba ayi wani abin- azo a gani ba, domin canza gwamnatin kasar.

Suna kuma bukatar ganin an gaggauta yiwa Mr. Mubarak da kuma sauran jami'an gwamnatinsa shari'a.