Kotu ta ce a biya diyya a Iraqi

Sojojin Birtani a Iraqi

Kotun Kare Hakkin bil Adama ta Tarayyar Turai ta umurci Biritaniya da ta biya dubun-dubatar daloli ga 'yan-uwan 'yan Iraqin da sojojin Biritaniya suka kashe yayin mamayar Iraqin.

A da dai Biritaniya ta dage ne akan cewa dokokin kare hakkin bil Adama na Turai ba su shafi sojojin da aka tura zuwa kasashen da ba sa cikin nahiyar turai ba.

Masu fafitikar kare hakkin bil Adama sun ce wannan muhimmin hukunci ne, ya kuma share hanya ga sauran 'yan Iraqi su nemi a yi masu adalci a kotunan Biritaniya.

Manema labarai sun ce zaa zura ido akan wannan hukunci a kasashe da dama wadanda sojojinsu suka taba aiki a kasar Iraqi.

Sojojin Birttaniyar ne dai suka bindige hudu daga cikin farar hullar da danginsu suka shigar da wannan kara.