Za'a rufe jaridar News of the World a Birtaniya

News of the World Hakkin mallakar hoto AP
Image caption News of the World

Kampanin buga jaridu na News International a Birtaniya, wanda ya samu kansa a tsaka mai-wuya game da zargin satar karanta ko sauraron sakonnin jama'a akan wayoyin salula ya ce zai rufe Jaridar News of the World.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da James Murdoch, shugaban kampanin, kuma dan Rupert Murdoch, hamshakin attajirin nan, ya fitar.

Sanarwar na cewar jaridar ta News of the World wadda za'a wallafa ranar lahadi ita ce bugon karshe.

Sai dai 'yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike akan zargin aikata ba daidai ba da ake yi wa jaridar.

Wasu fitattun 'yan siyasa na Birttaniya sun ce rufe gidan jaridar ta News of The World ba zai kawo karshen wannan dambarwa ba.