Shugaban kasar Nigeria ya rantsar da masu bashi shawara

Image caption Shugaba Jonathan

A Najeriya, shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya rantsar da mutum goma sha- uku daga cikin mutum ashirin da majalisar dattawan kasar ta amince ya nada su mukaman masu bashi shawara.

A jiya ne dai aka gudanar da bikin a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya na Abuja.

Tara daga ciki masu bada shawarar maza ne yayinda hudu daga ciki mata ne.

Sai dai sabanin yadda masu irin wannan mukami ke taka muhimmiyar rawa wajen yiwa shugabanni jagora a kasashen da suka ci gaba, a Najeriya wasu na kallon irin wadanda ake nadawa wadannan mukaman, a matsayin 'yan alfarma, amma masu rike da mukaman sun musanta hakan.

Senata Isiah Balat na daya daga cikin mutanen da aka rantsar kuma ya shaidawa BBC cewa ba haka lamarin yake ba, inda yace suna iya kokarinsu wurin bada shawarwarin inganta rayuwar al'ummar kasar.