A yau za'a sake gudanar da zanga zanga a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jakadan Amurka a Syria Robert Ford

Gwamnati da 'yan adawa a kasar Syria, kowanensu ya shirya kansa, akan yadda abubuwa zasu kasance bayan sallar juma'a ta yau, wacce a makonin baya- bayanan ta rika baiwa 'yan adawar damar gudanar da zanga- zanga akan tituna.

Hakazalika a ranar juma'a ce aka fi kashe masu zanga zangar nuna kyamar gwamnati sosai 'yanadawa sun ce gabakidaya masu zanga zanga dubu daya da dari uku sun rasu.

Babbar zanga zangar 'da i zuwa yanzu aka yi ita ce ta birnin Hama wadda akayi a ranar juma'ar data wuce.

Tun bayan wanan lokacin yansanda da sojoji na kokarin kama mutane a Hama kuma wasu mazauna birnin sun rika kafa shingaye inda suke amfani da duwatsu da kuma tayoyi domin su hanasu yin hakan.

Yayinda da ake sa ran yin fito na fito wasu mazauna sun fara tserawa daga birnin.

Sai dai jakadan Amurka a Syria Robert Ford ya wuce zuwa birnin na Hama .

Ma'aikatar huldar da kasashen waje ta Amurka ta ce yana son ya nuna goyon bayansa ga mazauna birnin.

Ta ce Mr Ford nada anniyar ganin ya tsaya a Hama domin ganin yadda zanga zangar wanan juma'ar zata kasance.