'Yan sanda sun tsare 'editan' News of The World

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Andy Coulson, tsohon editan jaridar News of the World

'Yan sanda a Landan sun ce suna tsare da Andy Coulson, tsohon editan jaridar News of the World, jaridar da ake wallafawa a ranar Lahadi wadda kuma za'a rufe saboda badakalar nadar bayanai da jaridar ta yi.

A wata sanarwa da 'yan sandan suka fitar, sun ce an kama Coulson ne saboda ana zarginsa da cin hanci da kuma batun satar bayanai.

Mista Coulson, wanda har wa yau tsohon daraktan yada labaran Fira Ministan Burtaniya David Cameron ne, ya musanta zargin, inda ya ce ba shi da masaniya kan batun nadar bayanan.

Tun farko dai Mista Cameron ya shaida wa wani taron manema labarai cewa, kan batun nadar bayanan ya ce ya dau alhakin nada Mista Coulson a matsayin daraktan yada labarai.

Shi dai Kamfanin News International ya yi shelar rufe jaridar News of the World, sakamakon cece- kucen da badakalar satar bayanan wayar salula ta janyo.

A ranar Lahadi mai zuwa ne dai za a buga jaridar ta karshe.

Shugaban kamfanin News International James Murdoch ya amince da cewa jaridar ta gaza gano musabbabin abin da ya kira kuran- kuran da ta rika maimaitawa .