An fara kai kayan abinci ta sama Somaliya

Wani yaro mai fama da tamowa a Mogadishu Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani yaro mai fama da tamowa a Mogadishu

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fara kai kayan abinci ta jirgin sama zuwa Mogadishu, babban birnin Somalia.

Hukumar ta kai tan goma na abinci mai kara kuzari daga Kenya don ciyar da yara kanana masu fama da bala'in yunwa.

Hukumar ta kuma ce za ta ciyar da yara dubu uku da dari biyar har na tsawon wata guda.

Kuma wannan shi ne sawun farko a sawu goman da aka shirya yi na kai kayan abincin ta sama.

Karin bayani