Kumbon Amurka ya yi tashin sa na karshe

Kumbon Amurka mai suna Atlantis Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Kumbon Amurka mai suna Atlantis

Jirgin jigila zuwa sararin samaniya na Amurka, ya tashi daga tashar Cape Canaveral a karo na karshe.

Dazu ne jirgin mai suna Atlantis ya tashi a tashar Florida.

Mai sanarwa a dakin kula zurga-zurgar jirgin jigilar ya sanarwar tashin jirgin na karshe zuwa sararin samaniya.

Ya ce; "A karo na karshe an kashe injinunan jirgin jigilar zuwa sararin samaniya, yayin da jirgin ya lula zuwa tafiyarsa ta karshe a tarihin tafiye-tafiyensa na tsawon shekaru talatin."

Wannan ne dai shine karon farko cikin fiye da rabin karni da Amurka ba ta da jirgin jigila ko wani kumbo zuwa sararin sama, sai dai ta nemi dani daga wajen Russia.