Norway za ta kafa kwamitin bincike

Jens Stoltenberg Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firayim Ministan Norway, Jens Stoltenberg

Firayim Ministan Norway, Jens Stoltenberg, ya bayar da sanarwar kafa wani kwamiti mai zaman kansa wanda zai binciki hare-haren da aka kai ranar Juma'a.

Kwamitin binciken zai duba yadda aka yi rayuka saba'in suka salwanta da kuma rawar da 'yansanda suka taka, ganin yadda ake zarginsu da sanyin jiki wajen kai dauki.

Firayim Ministan ya ce akwai dalilai da dama na kafa wannan kwamitin wadanda suka hada da samun bayani cikakke a kan abin da ya faru.

Abu ne mai matukar muhimmanci ga jama'a da iyalan wadanda abin ya shafa a ce an kammala binciken.

Za a yi wani biki na kasa don tunawa da wadanda suka mutu, kuma za a biya iyalan wadanda aka kashe diyya.