'Za a iya nasara kan kungiyar Al Ka'ida'

Leon Panetta
Image caption Sabon Sakataren Tsaron Amurka, Leon Panetta

Sabon sakateren tsaron Amurka, Leon Panetta, ya ce nasara a kan kungiyar Al Kaida abu ne da zai iya faruwa cikin dan gajeren lokaci.

Mista Panetta, wanda ke ziyararsa ta farko a Afganistan tun bayan kama aiki, ya nuna kwarin gwiwar cewa suna samun galaba.

Ya ce, "Tunda an gama da Osama bin Laden, yanzu mun gano wasu kushohin kungiyar Al Kaida a Pakistan da Yaman da sauran wurare.... kuma har idan za a iya hallaka su, to za a iya gurgunta kungiyar".