Anci tarar kamfanin pira ministan Italiya

Wata kotun daukaka kara a Italiya ta tace wani kamfanin, mallakar Pira ministan kasar ya biya diyyar dala miliyan dari 8 ga wani kamfani, saboda yankan bayan da yayi masa a wani cinikin hadewa tsakanin kamfanonin biyu da ya ci tura.

A kwanakin baya ne Pira Ministan kasar ya yi kokarin amincewa da wani kudirin doka da zai dakatar da hukuncin, amma dole tasa ya dakata saboda 'yan adawa sun yi masa caa.

Ana ganin wannan hukuncin dai wani koma baya ne ga Pira Ministan wanda gwamnatinsa ke fuskantar suka saboda matakan tsuke bakin aljihun da sukayi illa ga cibiyoyin kudin kasar.