Matar tsohon Shugaban Amurka Gerald Ford ta rasu

Hakkin mallakar hoto none

Matar tsohon Shugaban Kasar Amurka Gerald Ford wato Betty Ford ta rasu a Jihar California.

Ta rasu ne tana da shekaru 93 a duniya.

Betty ta yi fice a bangaren rashin gajiyawarta wajen yaki da shaye- shaye, sannan kuma ta kasance daya daga cikin matan Shugabannin Amurka da suka yi fice.

Betty ta kasance matar Shugaban Kasar Amurka bayan da aka maye gurbin Shugaba Richard Nixon da mataimakin sa.

A wani rubutu da ta yi ta ce wannan batu ne da Iyalinta sam basu so ba, wata dama kuma da ta amfani Amurka.

An dai jinjina mata, ita da mijinta Gerald Ford a saboda dawo da fata da suka yi a Shugabancin Kasar.

Basu dade da shiga Fadar White House ba aka gano cewa ciwon daji ya kama mata mama.

Tun kuma daga wannan lokacin ne ta kasance a sahun gaba wajen fafutukar yaki da ciwon dajin mama da kuma bincike kan gano shi akan lokaci.

Mace ce da ta goge akan batutuwa da dama, ciki har da sanin hakkokin mata, da dokokin zubar da ciki.

Ta kafa gidauniyar Betty Ford domin yaki da shaye shaye, bayan da ta yi maganin na ta sabon da ta yi da shan giya da kuma kwayoyi.

Nancy Reagan matar tsohon Shugaban Kasar Amurka Ronald Reagan dai ta bayyana Betty a matsayin macen da za'a yi koyi da ita.

Shugaba Ford ma da kansa ya taba yin wata karin magana makamanciyar cewa ana binsa bashi, ba ga namiji guda ba, sai ga mace guda, wato Matarsa.