Ana neman agajin abinci a Somalia

Yayinda farin da ake fama dashi a gabashin Afrika ke kara kamari, wata kungiyar agaji ta MSF ta ce ta gano cewa sansanonin masu bukatar agaji sai karuwa sukeyi a cikin Somalia.

Kakakin kungiyar ya shaidawa BBC cewa abun nada tada hankali matuka, domin zakaga mutane nata ficewa daga Habasha da Somalia saboda sun kai magaryar tukewa.

Anyi kiyasin cewa mutane miliyan goma ne dake ke fuskanatr yinwa yanzu haka.